Ta bayyana: Yadda rundunar sojin sama ta ragargaza mabuyar 'yan ta'adda a Borno

Ta bayyana: Yadda rundunar sojin sama ta ragargaza mabuyar 'yan ta'adda a Borno

- Rundunar sojin sama ta kasa (NAF) ta ce ta ragargaza mabuya da kuma wasu ababen hawan kungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP a Borno

- NAF ta ce ta lalata wasu kayayyaki a mabuyar kungiyar ISWAP da ke garin Tumbin Sale da Tumbin Allura dake kan iyakar tekun Chadi a jihar

- Rundunar ta dakarunta tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro, za su ci gaba dam kakkabe dukkanin 'yan ta'addan da suka yi saura a shiyyar Arewa maso Gabas

Rundunar sojin sama ta kasa (NAF) ta ce dakarun sintirinta na sama (ATF) da ke cikin atisayen LAFIYA DOLE, sun ragargaza wasu ababen hawan kungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP a garin Tumbin Sale da Tumbin Allura da ke Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojin saman, Air Commodore Ibinkunle Daramola, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Ya ce dakarun sojin na ATF sun kuma lalata wasu kayayyaki a mabuyar kungiyar ISWAP da ke garin Tumbin Sale da Tumbin Allura dake kan iyakar tekun Chadi a jihar.

KARANTA WANNAN: Ba zamu amince da sakamakon zaben Kaduna ba, sai INEC ta sake sabo - PDP

Ta bayyana: Yadda rundunar sojin sama ta ragargaza mabuyar 'yan ta'adda a Borno
Ta bayyana: Yadda rundunar sojin sama ta ragargaza mabuyar 'yan ta'adda a Borno
Asali: UGC

Daramola ya bayyana cewa rundunar ta gudanar da wannan aikin ne biyo bayan kwararan bayanai da suka samu da ke nuni da cewa akwai mayakan kungiyar ISWAP a cikin wasu motoci tare da kayan yaki da ke yawo a yankin.

"Akan hakan, jirgin yakin rundunar sojin sama tare da taimakon sashen leken asiri ISR, ya kai hari ga mabuyar 'yan ta'addan inda har aka samu nasarar lalata gine gine da kuma ababen hawarsu, wanda aka hango suna ci da wuta," a cewarsa.

Kakakin rundunar ta NAF, ya ce rundunar sojin tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro, za su ci gaba da zage damtse wajen ganin sun kakkabe dukkanin 'yan ta'addan da suka yi saura a shiyyar Arewa maso Gabas.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel