PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben gwamna a Borno

PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben gwamna a Borno

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) babin jihar Borno ta nuna rashin amincewa da sakamakon zaben gwamna wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar a jihar.

Sai dai kuma, jam’iyyun Action Peoples Party (APP) da Alliance of Social Democrats (ASD) sun sha alwashin mara wa gwamnatin APC mai zuwa baya dari-bisa-dari.

Kamfanin dillancin Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa NEC ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Farfesa Babagana Zulum, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da ya gudana a ranar Asabar.

PDP ta ki amincewwa da sakamakon zaben gwamna a Borno
PDP ta ki amincewwa da sakamakon zaben gwamna a Borno
Asali: UGC

Baturen zabe a jihar, Farfesa Alhassan Gani ya kaddamar da cewa Zulum ya samu kuri’u 1,175,440 inda ya kayar da Muhammad Imam na PDP wanda samu kuri’u 66, 117.

Gani yayi bayanin cewa zaben ya samu takarar jam’iyyun siyasa 32 a jihar.

KU KARANTA KUMA: PDP ta zama mafi rinjaye a majalisar dokokin Abia bayan lashe kujeru 19 cikin 24

A nashi martanin, Umar Bello, sakataren jam’iyyar, yace PDP ba ta amince da sakamakon zaben da INEC ta kaddamar ba saboda rashin bin ka’ida.

Bello, wanda ya kuma kasance wakilin jam’iyyar a cibiyar hada sakamakon zabe, yace bai sanya hannu a takardun da INEC ta kaddamar ba don yin zanga-zanga, inda ya kara da cewa jam’iyyar za ta sanar da matsayarta akan sakamakon.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel