Al’ummar garin Zaria sun bayyana farin cikin samun nasarar El-Rufai

Al’ummar garin Zaria sun bayyana farin cikin samun nasarar El-Rufai

Jama’an karamar hukumar Zaria ta jahar Kaduna sun yi fitar farin dango don murnar samun nasarar da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai yayi na sake lashe zaben gwamnan jahar a karo na biyu, inda suka tsayar da garin cak na tsawon awanni.

A ranar Litinin, 11 ga watan Maris ne hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da El-Rufai a matsayin zababben gwamnan jahar Kaduna, kamar yadda alkalumman sakamakon zaben daga kananan hukumomin jahar guda 23 suka nuna.

KU KARANTA: Abdulaziz Yari ne sanadiyyar samun nasarata – Inji zababben gwamnan jahar Zamfara

Al’ummar garin Zaria sun bayyana farin cikin samun nasarar El-Rufai
Yakin neman zaben El-Rufai
Asali: Facebook

Legit.ng ta ruwaito Nasir El-Rufai ne ya samu gagarumar nasara da bambamcin kuri’u 231, 173, bayan ya samu kuri’a 1,045,417, yayin da abokin karawarsa na jam’iyyar PDP, Isah Ashiru Kudan ya samu 814,244.

Majiyarmu ta ruwaito manyan titunan garin Zariya sun cika makil da jama’a, maza da mata, yara da manya suna murnar nasarar El-Rufai akan motoci dauke da wakokin gwamnan, wasu kuma na ta cashew abinsu, yayin da wasu suka fito daga gidajensu don baiwa idanunsu abinci.

Wani mazaunin garin Zaria, Mustapha Abubakar ya bayyana nasarar da El-Rufai a matsayin abin jin dadi da farin ciki ga shi kansa da ma iyalansa gaba daya, musamman yadda yace wasu na ganin idan babu su El-Rufai ba zai kai labari ba.

“Wannan nasara ta nuna makarytan banza ne, saboda mu mun yarda Allah ke bada mulki ga wanda Ya so a lokacin da yaso, kuma ya hana wanda Ya ga dama mulki.” Inji Malam Mustapha Zaria.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel