Ba zamu amince da sakamakon zaben Kaduna ba, sai INEC ta sake sabo - PDP

Ba zamu amince da sakamakon zaben Kaduna ba, sai INEC ta sake sabo - PDP

- Alhaji Isa Ashiru, dan takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam'iyyar PDP ya yi watsi da sakamakon zaben jihar

- Dan takarar gwamnan jihar karkashin PDP ya sha kasa a hannun gwamnan jihar mai ci a yanzu Nasiru E-Rufai, dan takarar jam'iyyar APC

- Ya lissafa kananan hukumomin da ya yi ikirarin an tafka kura kurai da suka hada da Giwa, Birnin Gwari, Kaduna ta Arewa, Igabi, Zaria, Lere da kuma Ikara

Alhaji Isa Ashiru, dan takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam'iyyar PDP ya yi watsi da sakamakon zaben jihar a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta kammala sanar da sakamakon zaben jihar a ranar Litinin.

Dan takarar gwamnan jihar karkashin PDP wanda ya sha kasa a hannun gwamnan jihar mai ci a yanzu Nasiru E-Rufai, dan takarar jam'iyyar APC, ya ce yana da kwararan hujjoji da ke nu ni da cewa an tafka magudi a zaben jihar.

Ya yi kira da a soke sakamakon zaben jihar, yana mai ikirarin cewa an tafka kura kurai a wasu kananan hukumomi na jihar A cewarsa, rahotannin da wakilan jam'iyyarsu suka tattara ya bayyana cewa an karya ka'idojin zabe a jihar.

KARANTA WANNAN: PDP ta zama mafi rinjaye a majalisar dokokin Abia bayan lashe kujeru 19 cikin 24

Ba zamu amince da sakamakon zaben Kaduna ba, sai INEC ta sake sabo - PDP
Ba zamu amince da sakamakon zaben Kaduna ba, sai INEC ta sake sabo - PDP
Asali: Twitter

"Akan wannan dalilan ne na kura kuran da aka tafka a wajen zaben ya sa jam'iyyarmu a cikin wata takardar korafi da ta aikewa hukumar INEC da ke a jihar, mun yi watsi da wannan sakamakon zabe, tare da bukatar hukumar ta soke sakamakon.

"Yana da kyau ku sani cewa akwai rahotanni da muka samu na cewa ba a yi amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a a wasu rumfuna da dama ba," a cewar sa.

Dan takarar gwamnan karkashin PDP ya lissafa kananan hukumomin da ya yi ikirarin an tafka kura kurai da suka hada da Giwa, Birnin Gwari, Kaduna ta Arewa, Igabi, Zaria, Lere da kuma Ikara.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel