A daina amfani da addini wajen gwara kan jama’a inji El-Rufai

A daina amfani da addini wajen gwara kan jama’a inji El-Rufai

Mai girma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, wanda ya lashe zaben da aka yi kwanan nan, ya godewa mutanen da su ka fito su ka sake zaben sa a karo na biyu domin ya zarce a kan mulki.

A jawabin godiyan da gwamnan na Kaduna yayi, ya nemi mutane su guji amfani da harkar siyasa wajen cin ma burin siyassa da neman abin Duniya. Gwamna Nasir El-Rufai yace bai kamata addinin jama’a ya rika fitowa fili ba.

Malam Nasir El-Rufai yana ganin cewa ba daidai bane addini ya zama silar dakile cigaban al’umma ba. Gwamnan har wa yau, ya kuma bayyana cewa zai yi kokarin hada-kan dukannin al’ummar jihar kamar yadda doka tace.

El-Rufai a jawabin da yayi, ya nemi a zauna lafiya da juna ba tare da cusa kiyayya ko zargi a tsakani ba, gwamnan da ya samu tazarce yake cewa asalin kowa a Duniya daga Adamu ne da Nana Hauwa, don haka dole a mutunta juna.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta doke PDP a zaben Gwamna na Jihar Kaduna

A daina amfani da addini wajen gwara kan jama’a inji El-Rufai
Gwamna El-Rufai ya godewa Mutanen Kaduna na sake zaben sa
Asali: UGC

Gwamnan yake cewa ko da yayi takara ne a APC, amma yanzu ya zama Gwamnan kowa da kowa a jihar Kaduna don haka ya sake cin burin inganta harkar kiwon lafiya da ilmi, tare da kuma kawar da matsanancin talauci a jihar.

Nasir El-Rufai ya nuna cewa ba zai bata lokaci yana fama da murnar lashe zabe ba, inda yace zai maida hankali ne wajen cigaba da ganin Matasa sun samu aikin yi kuma an samu sauki ta fuskar tsaro domin ganin bai bada kunya ba.

Gwamnan na APC ya kuma jinjinawa mutanen jihar da su ka zabe sa tare da Abokiyar takarar sa, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, wanda a tarihin Arewacin Najeriya ba a taba samun macen da ta rike wannan babban matsayi ba sai yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel