An damke wanda ake zargi da kashe dan majilisar tarayya a Oyo

An damke wanda ake zargi da kashe dan majilisar tarayya a Oyo

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewa ta kama wanda ake zargi da kashe dan majalisar tarayya na jihar Oyo, Temitope Olatoye wato Sugar

- Mataimakin Sufeta Janar da Kwamishinan 'yan sanda na jihar ne suka bayar da sanarwar sai dai basu fadi sunansa ba

- Yan sandan sun ce suna da cikaken hujja da bayanai da ke nuna shine ya aikata kisar sai dai har yanzu ba a kammala bincike ba

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Oyo ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da hannu cikin kisar dan majalisar tarayya mai wakiltan Akinyele/Lagelu mai suna Temitope Olatoye wanda ake yiwa lakabi da Sugar.

Zabe: An damke wanda ake zargi da kashe dan majilisar Oyo da ake kashe
Zabe: An damke wanda ake zargi da kashe dan majilisar Oyo da ake kashe
Asali: Twitter

Mataimakin Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya mai kula da zone 11, Leye Oyebade da Kwamishinan 'yan sandan jihar Oyo, Shina Olukolu ne suka bayyana hakan a jiya Litinin.

A yayin da suka yiwa manema labarai bayani, shugabanin 'yan sandan biyu sun ce kashe Mr Olatoye ba shi da alaka da zaben gwamnan da 'yan majalisun jiha da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

DUBA WANNAN: Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja

Sun ce an kama mutane 18 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar, an kuma samu bindigu shida, alburusai tara, adda da wukake daga wurin wadanda ake zargi da aikata laifukan.

Duk da cewa ba su fadi sunan wanda ake zargin ba, sun hakikance da cewa 'yan sanda suna da isasun hujoji da bayanai da suka kai ga kama wanda ake zargin.

Sun ce sashin binciken manyan laifuka wato SCIID suna cigaba da bincike a kan lamarin.

Mr Oyebade ya ce, "Mun kama wani da muke zargi amma ba zamu iya bayar da cikaken bayani a kansa ba. Na ziyarci asibitin koyarwa na Ibadan tare da kwamishinan 'yan sanda na jihar Oyo a ranar Asabar. Shugaban asibitin shima yana tare da mu.

"Muna kyautata zaton kisar ba ta da alaka da zaben da aka gudanar a ranar Asabar duba da inda abin ya faru da bayanan da muka samu akan abinda ya faru kafin harin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel