Jihohin Bauchi, Kano, Sokoto, Rivers da sauransu za su san makomarsu yau - INEC

Jihohin Bauchi, Kano, Sokoto, Rivers da sauransu za su san makomarsu yau - INEC

- A yau ne ake sa ran INEC, za ta kawo karshen rudanin da ya mamaye zaben gwamna na wasu jihohi da ta bayyana zabensu a matsayin wanda bai kammala ba

- Ana sa ran INEC za ta sanya ranar sake gudanar da zaben, musamman a jihohin Adamawa, Bauchi, Benue, Kano, Sokoto, Rivers, Filato da kuma sauransu

- Hukumar na da wa'adin kwanaki 21 ta kammala zabukan dukkanin yankuna da jihohin da aka bayyana zabensu a matsayin zaben da bai kammala ba

A yau ne ake sa ran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, za ta yi wani muhimmin zama kan kawo karshen rudanin da ya mamaye zaben gwamnoni na wasu jihohi da hukumar ta bayyana zabensu a matsayin wanda bai kammala ba.

Wata babbar majiya daga hukumar INEC ta shaidawa jaridar LEADERSHIP a ranar Litinin cewa kusoshin hukumar zaben za su hadu a yau domin yanke hukunci kan zabukan da ba a kammala ba da kuma sanya ranar da za a sake gudanar da zaben, musamman a jihohin Adamawa, Bauchi, Benue, Kano, Sokoto, Rivers, Filato da kuma sauran jihohin da aka soke zabensu.

Hukumar na da wa'adin kwanaki 21 ta kammala zabukan dukkanin yankuna da jihohin da aka bayyana zabensu a matsayin zaben da bai kammala ba.

KARANTA WANNAN: Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, CP Wakili ya zama gwarzon zaben 2019

Jihohin Bauchi, Kano, Sokoto, Rivers da sauransu za su san makomarsu yau - INEC
Jihohin Bauchi, Kano, Sokoto, Rivers da sauransu za su san makomarsu yau - INEC
Asali: Twitter

Jihohin na daga cikin jihohi 29 na kasar da aka gudanar da zaben gwamnoninsu a ranar Asabar 9 ga watan Maris amma aka ki sanar da sakamakon zabensu ko kuma dan takarar da ke kan gaba bai samu kuri'u mafi yawan kuri'un da aka soke ba wanda ya zama tilas a sake gudanar da zabe.

A wani lamarin kuma, idan aka samu yawan kuri'un da aka kada da kuri'un da dan takarar da ke kan gaba ya samu ba suna kasa da kuri'un da aka soke, to a nan ma ya zama wajibi a sake gudanar da zabe.

Sai dai, jihohin da ba a gudanar da zaben gwamna ba sun hada da Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Kogi, Ondo da Osun, sakamakon wa'adin gwamnonin da ke kan mulki a yanzu bai kare ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel