Abdulaziz Yari ne sanadiyyar samun nasarata – Inji zababben gwamnan jahar Zamfara

Abdulaziz Yari ne sanadiyyar samun nasarata – Inji zababben gwamnan jahar Zamfara

Sabon zababben gwamnan jahar Zamfara, Alhaji Mukhtar Idris ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari, wanda ya danganta nasarar dsaya samu kacokan ga Gwamna Yari sakamakon gudunmuwar daya bashi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mukhtar ya bayyana haka ne a gidan iyayensa dake garin Gusau na jahar Zamfara, inda yake mika godiyarsa ga dimbin al’ummar Zamfara da suka bashi goyon baya, ta hanyar zabensa a matsayin gwamnansu.

KU KARANTA: Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 13, PDP ta samu nasara a jahohi 9

Abdulaziz Yari ne sanadiyyar samun nasarata – Inji zababben gwamnan jahar Zamfara
Mukhtar
Asali: UGC

Haka nan sabon gwamnan yayi alkawarin tafiya da mata da matasa a sha’anin mulkinsa tare da basu fifiko, sa’annan ya kara da cewa tunda daga shi har mataimakinsa duk matasa ne, tabbas zasu yi amfani da matasa yadda ya kamata.

“Ina godiya matuka ga shugabanmu, kuma babban gwamnan Najeriya, Alhaji Abdulaziz Yari bisa tsayin dakan da yayi don ganin wannan nasara ta tabbata, hakan kuma ya tattara ne ga jajircewarsa, dagiya, kwarewa, hakuri, sanin ya kamata da kuma martaba doka da oda, da haka muka kai wannan matsayi.

“Ina gode ma Allah, sa’annan ina tabbatar ma gwamnan cewa ba zan bashi kunya ba, musamman ta bangaren ciyar da jahar gaba.” Inji shi.

Babban baturen zaben gwamnan jahar Zamfara, Farfesa Kabiru Bala ne ya sanar da sunan Mukhtar Idris a matsayin wanda ya lashe zaben jahar Zamfara da kuri’u 534, 541, inda ya kayar da Bello Matawalle na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’a 189,452.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel