Tambuwal ya fara banbami bayan INEC tace ba a kammala zabe ba

Tambuwal ya fara banbami bayan INEC tace ba a kammala zabe ba

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto yayi watsi da matakin da hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC ta dauka game da zaben gwamna da aka yi a jihar a karshen makon da ya gabata.

Aminu Waziri Tambuwal ya nemi hukumar INEC tayi maza ta sanar da cewa shi ne kurum ya ci zabe a jihar Sokoto. INEC dai ta dage zaben jihar ne bayan ta duba ta ga cewa tazarar da ke tsakanin manyan jam’iyyun bai da yawa.

Hukumar INEC ta bayyana cewa ratar kuri’a 3, 413 ne rak gwamna Aminu Tambuwal ya ba ‘dan takarar jam’iyyar APC watau Aliyu Ahmed. Haka kuma akwai kuri’u fiye da 75, 403 da aka soke zaben gwamnan da aka yi a cikin jihar.

KU KARANTA: ‘Dan takarar Shugaban kasa ya samu kuri’a 100, 000 a sama

Tambuwal ya fara banbami bayan INEC tace ba a kammala zabe ba
Gwamnan Jihar Sokoto mai-ci Aminu Tambuwal yana bakin aiki
Asali: Depositphotos

Gwamna Tambuwal da yake jawabi ga mutanen sa, yace a tsarin mulki da dokar kasa babu wani abu mai kama da cewa an kammala zabe amma ba a karasa ba don haka yake ganin akwai bukatar a shiga kotu da hukumar INEC din.

A jawabin na gwamnan jiya ya nemi INEC ta sake duba wannan mataki da ta dauka, yana mai gargadin cewa babu wanda ya isa ya murdewa jama’a zaben da su kayi. Gwamnan ya kuma yi kira da jama’a su sake fita a ranar wani zaben.

Sadiq Musa wanda shi ne malamin zaben jihar ya bayyana cewa yawan kuri’un da aka soke ne a fadin jihar ya sa dole za a kara yin wani zaben domin tantance wanda yayi nasara. ‘Dan takarar APC ya ji dadin wannan mataki da aka dauka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel