Gaskiya-da-gaskiya: Hukumar INEC ta bayar da umurnin a kama jami'in ta a wata jihar APC

Gaskiya-da-gaskiya: Hukumar INEC ta bayar da umurnin a kama jami'in ta a wata jihar APC

Jami'an tsaro sun cafke wani jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC dake da alhakin tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Ohaji Egbema ta jihar Imo mai suna Kelechi Ezirim saboda zargin samun sa da laifin tafka magukin zabe.

Kamar yadda muka samu, hukumar zaben ce ta INEC ta bayar da umurnin kama shi ta kuma tare da wani jami’in mai kula da yankin Ohaji Egbema mai suna Chris Ogbuadu wanda dai tuni ‘yan sanda suka yi awon gaba da su.

Gaskiya-da-gaskiya: Hukumar INEC ta bayar da umurnin a kama jami'in ta a wata jihar APC
Gaskiya-da-gaskiya: Hukumar INEC ta bayar da umurnin a kama jami'in ta a wata jihar APC
Asali: Original

KU KARANTA: Arewa na bukatar jagora irin Kwankwaso - Sheikh Ibrahim Khalil

Legit.ng Hausa ta samu cewa lamarin ya faru ne jim kadan da jam’in zaben suka gabanar da sakamakon zaben a daidai lokacin da wakilan jam’iyuu ke nuna rashin amincewarsu da sakamakon da ya gabatar.

Dukkan jami’an sun amince da laifin hada sakamakon zaben da na wuraren da ba a yi zabe gaba daya ba.

Mista Ezirim ya ce, an sanar da shi cewa, wasu yan bangar siyasa sun kwace kayan zaben wasu mazabu amma kuma daga baya ya karbi sakamakon zabe daga wadannan mazabun da aka sace kayan zabansu.

Babban jami’in zaben yankin, Francis Otunta, ya bayyana wannan halayar nasa a matsayin yunkurin yin magudi ya kuma bayar da umurnin kama jami’an guda biyu nan take.

Daga nan ne aka ci gaba da aikin tattara sakamakon zaben bayan da aka dan dakatar da aikin da sanyin safiyar Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel