Sakamakon zabe: Gwamnan jahar Taraba ya zarce

Sakamakon zabe: Gwamnan jahar Taraba ya zarce

Gwamnan jahar Taraba, Darius Ishaku daya sake tsayawa takarar gwamnan jahar a inuwar jam’iyyar PDP ya lashe zaben daya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, wanda hakan ya bashi damar zarcewa akan madafan iko daga nan har shekarar 2023.

Babban baturen zabe na jahar, Farfesa Shehu Iya ne ya sanar da sakamakon zaben da safiyar Litinin a babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC dake garin Jalingo, inda yace Gwamna Darius ya samu kuri’a 520, 433.

KU KARANTA: Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 13, PDP ta samu nasara a jahohi 7

Yayin da dan takarar gwamnan jahar a inuwar jam’iyyar APC, Sani Danladi ya samu kuri’a 362, 735, wannan nasara da jam’iyyar PDP ta samu na nufin zata cigaba da mulkin jahar data faro tun a bayan dawowar Najeriya turbar Dimukradiyya a shekarar 1999.

Legit.ng ta ruwaito jahar Taraba na da kananan hukumomi goma sha shida, kuma wasu daga cikin kananan hukumomi goma sha biyu da Darius yaci sun hada da Sardauna, Takum, Zing, Yorro, Kai, Bali, Donga, Wukari, Gashaka, Kurmi da kuma Ussa.

Shi kuwa Alhaji Sani Danladi ya lashe kananan hukumomi guda hudu da suka hada da Jalingo, Gassol, Ibbi da kuma karamar hukumarsa ta Karim Lamido.

Babban karamar hukumar da Danladi yafi samun kuri’a itace karamar hukumar Jalingo, inda ya samu kuri’a 58,511, yayin da Darius Ishaku ya samu 31,917. Shi kumwa Darius ya fi samun kuri’a a Takum, inda ya samu 50, 562, shi kuma Danladi ya samu 14, 014.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel