Adadin kuri'u da aka soke ya haura tazarar da ke tsakanin Abba da Ganduje - INEC

Adadin kuri'u da aka soke ya haura tazarar da ke tsakanin Abba da Ganduje - INEC

Bayan tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 44 na jihar Kano a jiya Litinin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta kaddamar da cewa sai an sake gudanar da zabe a mazabun wasu kananan hukumomi na jihar.

Hukumar INEC ta kaddamar da cewa zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata bai kammala ba sakamakon yadda manyan 'yan takara biyu na jam'iyyar PDP da kuma APC suka rike wuta a tsakanin su.

Dan takarar gwamnan jihar a karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya samu gamayyar kuri'u 1,020,465, yayin da babban abokin adawar sa na jam'iyyar APC, gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya lashe kuri'u 987,459.

Adadin kuri'un da aka soke ya haura tazarar da ke tsakanin Abba da Ganduje - INEC
Adadin kuri'un da aka soke ya haura tazarar da ke tsakanin Abba da Ganduje - INEC
Asali: UGC

Bisa ga tanadi na doka da kuma shari'a, babban Baturen zabe na jihar Farfesa Riskuwa Shehu ya bayyana cewa, zaben jihar bai kammala ba sakamakon yadda adadin kuri'u da aka soke a wasu mazabu ya haura tazarar da ke tsakanin gwamna Ganduje da abokin adawar sa na jam'iyyar APC.

Farfesa Shehu ya yi fashin baki da cewar adadin kuri'u 128,572 da aka soke ya haura tazara ta adadin kuri'u 33,006 da ke tsakanin manyan 'yan takarar masu hankoron samun nasara. Ya ce adadin kuri'u da aka soke kan iya sauya alkaluman zabe wajen tabbatar da rinjayen nasara a tsakanin 'yan takara.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Cikin zayyana dalilai na soke wasukuri'u, Farfesa Shehu wanda ya kasance shugaban Jami'ar jihar Kebbi ya ce, hakan ya bayu ne sakamakon hargitsi da kuma maimaicin kada kuri'u da suka auku a wasu mazabu cikin kananan hukumomi 22 da ke jihar Kano.

Ya ce wannan lamari na sake zabe zai shafi rumfunan zabe 172 da ke fadin jihar Kano inda hargitsi ko maimaicin kada kuri'u ya gudana yayin zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel