Wata Kungiya na so Sanata Ahmad Lawan ya zama Shugaban Majalisa

Wata Kungiya na so Sanata Ahmad Lawan ya zama Shugaban Majalisa

Mun ji cewa Kungiyar NIPF watau National Interest Progressive Forum, tayi kira ga jam’iyyar APC mai mulki da ta goyi bayan Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa a bana.

Kungiyar tayi kira ga APC da ta tsaida Sanata Ahmad Lawan mai wakiltar Yobe ta Arewa a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya. Shugaban wannan kungiya ta NIPF da kuma Sakataren sa su kayi wannan jawabi.

Ibrahim Sadiq Taura wanda shi ne shugaban NIPF da kuma Clement Ojima, wanda yake rike da mukamin Sakatare, sun fitar da bayani a makon nan inda su kace akwai bukatar APC ta zabi Lawan a matsayin shugaban majalisa.

KU KARANTA: Buhari ya yi gum da bakinsa game da rikicin siyasar Kano

Wata Kungiya na so Sanata Ahmad Lawan ya zama Shugaban Majalisa
An nemi Buhari ya sa baki a game da zaben Shugabannin Majalisa
Asali: Depositphotos

Kungiyar tace tayi la’akari ne da biyayyar da ‘dan majalisar yayi wa jam’iyya tun fil azal. Haka kuma Alhaji Ibrahim Sadiq Taura da Sakataren na sa, sun yi kira ga APC ta tsaida shugaba mai matukar biyayya a majalisar wakilai.

Wannan ne zai ba majalisa damar yin aiki cikin sauki da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. Kungiyar ta NIPF ta na kuma so shugaban kasa ya sa baki wajen zaben wadanda su ka dace su jagoranci ragamar majalisar Najeriya.

A 2015 dai shugaba Muhammadu Buhari ya zare hannun-sa daga rikicin majalisa inda yace kowa na sa ne. Wannan abu ya jawowa gwamnatin jam’iyyar mai mulki cikas a wa’adin farko inji kungiyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel