Kuma dai: An hallaka mutane 16 a jihar Kaduna - hukumar Yan sanda

Kuma dai: An hallaka mutane 16 a jihar Kaduna - hukumar Yan sanda

Hukumar yan sandan jihar Kaduna a ranar Litinin ta tabbatar da cewa akalla mutane 16 sun rasa rayukansu a kauyen Barde dake Maro, karamar hukumar Kajuru.

Kakakin hukumar yan sandan, Yakubu Sabo, ya tabbatar da hakan en ga hukumar dillancin labaran Najeriya a Kaduna.

Sabo ya ce misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Lahadi, wasu yan bindiga suka shiga kauyen Barde dake Maro, kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi kuma akalla mutane 16 suka rasa rayukansu.

Yace da hukumar ta samu labarin, an tura jami'an tsaro karkashin jagorancin DPO na Kajuru tare da sojoji domin damke wadanda suka aikata wannan ta'asa. Kana an kwantar da kura yanzu haka.

KU KARANTA: Hukumar sojin sama ta ragargaji yan Boko Haram a Tumbun Sale da Tumbun Allura

Yace: "Yayinda ake cigaba da bincike, kwamishanan yan sanda, Ahmad Abdurrahman, ya lashi takobin bayyana wadanda suka dauki nauyin wannan mumunan aiki zasu bayyana gaban hukuma."

Ya yi kira da mutan jihar su kwantar da hankulansu kuma ya mikan sakon ta'aziyarsa ga wadanda abun ya shafa.

Wani mazaunin garin Dogon Noma yace: "Abin ya fara ne misalin karfe 7 na safe. Sai suka fara jin harbe-harbe. Sun raba kawunansu uku, yayinda kashi daya ke cikin daji, sauran biyun sun shiga cikin garin.

Kashi na farko sue harbe-harbe. Da mutane suka fara guduwa, sai kashi na biyun suka fara kona gifajen mutane. A kauyen gaba daya, babu gidan da basu bankawa wuta ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel