Akwai abin tarihu guda daya da zan kafa a Najeriya – Buhari

Akwai abin tarihu guda daya da zan kafa a Najeriya – Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wani muhimmin tarihi guda daya tilo da ya ke son kafa wa a Najeriya.

- Buhari ya bayyana cewar babban burin sa shine ake tuna shi a matsayin mutumin da assasa tushen gudanar da zaben gaskiya a Najeriya

- Shugaban kasar ya yi wannan kalami ne a yau Litinin, 11 ga watan Maris, yayin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar bashi da wani buri da ya wuce ake tunashi a matsayin mutumin da ya cika alkawarin bawa ‘yan Najeriya damar zaben shugabannin da su ke so ta hanyar gudanar da sahihin zabe na gaskiya.

Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya bayyana cewar Buhari ya yi wannan furuci ne yayin karbar bakuncin gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a gidan sa da ke garin Daura.

Masari ya ziyarci Buhari a Daura ne domin nuna ma sa sakamakon zaben kujerar gwamna da ya lashe.

Shugaba Buhari yay aba wa ‘yan Najeriya bisa yadda su ka fita su ka kada kuri’un su a zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Akwai abin tarihu guda daya da zan kafa a Najeriya – Buhari
Buhari da Masari
Asali: UGC

Da ya ke Magana a kan yadda aka gudanar da zaben cikin nasara da zaman lafiya, shugaba Buhari ya ce; “na sha fada cewar dole zabe ya kasance na gaskiya, dole a bar jama’a su zabi duk wanda su ke so.

“Na yi farinciki cewar ‘yan Najeriya sun fahimce ni kuma sun yi aiki da shawara ta. Ikon zaben shugabannin a hannun jama’a ya ke, ba kuma da karfi ake samun mulki ba.

DUBA WANNAN: Ta tabbata: Zidane ya maye gurbin Solari a Real Madrid

“Dole wadanda aka zaba su kasance ma su adalci. Ni shine tarihin da nake burin na bari a

Najeriya."

Masari ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Katsina a karo na biyu da kuri’u 1,178,864 yayin da babban abokin hamayyar sa na jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado, ya zo na biyu da adadin kuri’u 488,621.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel