Ruwan wuta: Hukumar sojin sama ta ragargaji yan Boko Haram a Tumbun Sale da Tumbun Allura

Ruwan wuta: Hukumar sojin sama ta ragargaji yan Boko Haram a Tumbun Sale da Tumbun Allura

Hukumar sojin saman Najeriya ta ce jami'an Operation Lafiya Dole ta ragargaza sansani da motocin yan kungiyar daular Musulunci a yankin Afrika maso yamma wato ISWAP a Tumbun Sale da Tumbun Allura.

Kauyukan biyu a soji suka kai harin na kusa da tafkin Chadi dake jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

Jawabin da kakakin hukumar, Air Commodore Ibikunle Daramola, yace an kai wadannan hare-hare ne a ranar 8 ga watan Maris, 2019 bisa ga binciken leken asiri da ke nuna cewa yan ta'addan suna boye a wajen.

Yace: "Jirgin hukumar sojin sama Alpha Jet, tare da goyon bayan sashen ilimin leken asirin, ta tashi domin kai gari ga wasu wuraren da yan ta'adda ke boye inda aka samu nasarar ragargazan gidajensu da kuma kona motarsu daya."

KU KARANTA: Da duminsa: An sanya dokar ta baci a jihar Taraba

Mun kawo muku rahoton cewa dakarun rundunar hadaka ta Sojojin kasashen yankin tafkin Chadi, MNJTF, sun samu gagarumar nasara akan mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a wasu samame da suka kai musu da kuma karanbatta daban daban da suka yi tsakaninsu.

Kaakakin MNJTF, Kanal Timothy Antigha ne ya sanar da haka a daren Asabar, 9 ga watan Maris inda yace Sojojin sun kashe yan Boko Haram guda Arba’in a yayin dauki ba dadin da suka yi, hare haren da yace sun kwashe tsawon kwanaki goma suna kaiwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel