Da duminsa: An sanya dokar ta baci a jihar Taraba

Da duminsa: An sanya dokar ta baci a jihar Taraba

Gwamnatin jihar Taraba a ranar Litinin ta sanya dokar ta baci a Jalingo, babbar birnin jihar har lokacin da ubangiji ya so.

Game da cewar sakataren labaran gwamnan jihar, Hassan Mijinyawa, an sanya dokar hana fitan ne daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe.

Amma gwamnatin ta kara da cewa an togaciye wasu jami'an hukumar INEC, jami'an jam'iyyun siyasa da masu lura da zabe. Wannan na nufin cewa za'a barsu su fita aiki a wannan lokaci.

Mr Ishaku ya yi kira ga mutan jihar da su cigaba da kasancewa masu bin doka kuma ya yi kira ga jami'an tsaro su tabbatar an bi wannan doka.

Hukumar dillancin labaran Najeriya ta bayyana cewa an saki sakamakon kananan hukumomi takwas a yanzu kuma jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta lashi bakwai, yayinda All progressives Congress, APC, ta samu daya kacal.

Har yanzu ana hada sauran sakamakon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel