A sanar da sakamakon zaben Kano kafin Sallar Isha'i - Wakil

A sanar da sakamakon zaben Kano kafin Sallar Isha'i - Wakil

- Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mohammed Wakili ya bayar da umurnin cewa a sanar da sakamakon zaben jihar Kano kafin Sallar Isha'i

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale wajen bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano wanda ake yiwa inkiya da maza kwaya, mata kwaya, Mohammed Wakili ya bayar da umurnin cewa a sanar da sakamakon zaben jihar Kano kafin Sallar Isha'i kamar yadda shafin BBC Hausa ta ruwaito..

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun kalubale dangane da bayyana sakamakon zaben jihar.

A sanar da sakamakon zaben Kano kafin Sallar Isha'i - Wakil
A sanar da sakamakon zaben Kano kafin Sallar Isha'i - Wakil
Asali: UGC

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakil, ya shiga bayan labule a halin yanzu tare da babban Bature kuma Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu.

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, a halin yanzu ana can ana ci gaba da kus-kus tsakanin kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakil da kuma babban Bature kuma kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Shehu.

KU KARANTA KUMA: Aiki ya kawo ni sai dai ku kashe ni - Kwamishinan zaben Kano

Ba bu masaniya dangane da dalilin wannan ganawa ta sirrance da ke wakana cikin gaggawa kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel