Aiki ya kawo ni sai dai ku kashe ni - Kwamishinan zaben Kano

Aiki ya kawo ni sai dai ku kashe ni - Kwamishinan zaben Kano

- Kwamishinan zaben jihar kano ya ce sai dai a kashe shi a kan aikinsa amma ba zai fasa bin tsari ba

- Hakan ya biyo bayan gumurzun da ake kan yi ne tsakanin magoya bayan jam' iyyun siyasa a jihar

Kwamishinan zaben jihar kano, Farfesa Ristuwa Arabu Shehu ya ce sai dai a kashe shi a kan aikinsa amma ba zai fasa bin tsari ba. A cewarsa aiki ne ya kawo shi jihar don haka ya zama dole ya aiwatar da hakan.

Aiki ya kawo ni sai dai ku kashe ni - Kwamishinan zaben Kano
Aiki ya kawo ni sai dai ku kashe ni - Kwamishinan zaben Kano
Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan gumurzun da ake kan yi ne tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyun siyasa a jihar wato tsakanin mabiya jam' iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da na All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar

Yace: “Ni idan ms kasheni za ku yi kuyi, aiki ne ya kawo ni nan babu wani zancen siyasa ina fada maku, ya kamata ace akwai bin ka’ida anan.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zulum na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Borno

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zabed mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da cewar sakamakon zaben gwamna a jihar Kano na nan daidai kuma babu abunda zai same shi.

Mutane na cikin halin fargaba kan tsawon lokacin da aka dauka ba a sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa ba dake jihar.

Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Ristuwa Arabu Shehu, ya bayar da tabbacin yayinda yake jawabi ga manema labarai kan rigimar da ke tattare da dogon lokacin da aka dauka wajen hada sakamakon zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel