Yanzu Yanzu: Zulum na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Borno

Yanzu Yanzu: Zulum na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Borno

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da Farfesa Babagana Umara Zulum na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Borno.

Farfesa Zulum ya samu kuri’u 1,175,440 inda ya doke babban abokin adawarsa Mogammed Alkali Imam na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya samu kuri’u 66,115.

Baturen zaben gwamnan, Farfesa Alhassan Mohammed Gani, Shugaban jami’ar tarayya Kashere, jihar Gombe, ya bayar da adadin masu rijista a jihar matsayin 2,316,218 sannan an tantance mutane 1,292,138.

Yanzu Yanzu: Zulum na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Borno
Yanzu Yanzu: Zulum na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Borno
Asali: Getty Images

Ya bayar da dukka adadin kuri’un da aka kada a matsayin 1,289,027; kuri’un masu inganci sun kasance 1,266,967 sannan an soke kuri’u 22,060.

Baturen zaben yace jam' iyyun siyasa 32 ne suka shiga zaben.

KU KARANTA KUMA: Babu abunda zai samu sakamakon zaben gwamnan Kano - INEC

Kafin kaddamar da wanda yayi nasara, dukkanin wakilan jam' iyyun siyasan sun sanya hannu a sakamakon zaben.

"Farfesa Babagana Umara Zulum na jam' iyyar APC, bayan ya cika dukkanin abubuwan da doka ta tanadar, an kaddamar da shi a matsayin wanda ya laashe zabe," kamar yadda Farfesa Gani ya sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel