Dalilin da ya sa aka saki mataimakin gwamnan Kano

Dalilin da ya sa aka saki mataimakin gwamnan Kano

A safiyar yau Litinin, 11 ga watan Maris ne aka saki mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Gawuna bayan an kama shi ranar Lahadi, 10 ga watan Maris da dare bisa zarginsa da yunkurin tafka magudin zabe.

An zargi Gawuna da shi da kwamishinan kananan hukumomin jihar da kekketa sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa.

An dai saki mataimakin gwamnan ne dalilin kariya da yake da ita a matsayinsa na mataimakin gwamna.

Sai dai sauran mutanen da aka kamasu tare na nan tsare har yanzu a hannun 'yan sanda.

Wasu kwararru a fannin shari'a sun bayyana cewa hukumar 'yan sanda ba ta da hurumin kama mutum mai irin mukaminsa.

Dalilin da ya sa aka saki mataimakin gwamnan Kano
Dalilin da ya sa aka saki mataimakin gwamnan Kano
Asali: Facebook

A bis ga sashi na 308, sakin layi na daya da na biyu da na uku, jami'an tsaro ba su da ikon kama shugaban kasa da mataimakinsa, ko gwamna da mataimakinsa.

KU KARATA KUMA: Babu abunda zai samu sakamakon zaben gwamnan Kano - INEC

Haka zalika ba su da karfin da za su iya gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma su gabatar da babba ko karamin laifi a kansa a gaban kowace irin kotu.

Sai dai daga baya rundunar 'yan sandan ta ce ba kama shi ta yi ba inda a cewarta kubutar da shi ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel