Babu abunda zai samu sakamakon zaben gwamnan Kano - INEC

Babu abunda zai samu sakamakon zaben gwamnan Kano - INEC

Hukumar zabed mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da cewar sakamakon zaben gwamna a jihar Kano na nan daidai kuma babu abunda zai same shi.

Mutane na cikin halin fargaba kan tsawon lokacin da aka dauka ba a sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa ba dake jihar.

Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Ristuwa Arabu Shehu, ya bayar da tabbacin yayinda yake jawabi ga manema labarai kan rigimar da ke tattare da dogon lokacin da aka dauka wajen hada sakamakon zaben.

Babu abunda zai samu sakamakon zaben gwamnan Kano - INEC
Babu abunda zai samu sakamakon zaben gwamnan Kano - INEC
Asali: Depositphotos

Ya bayar da tabbacin cewa hukumar za ta yi adalci wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Shehu ya jadadda cewa INEC za ta sake harhada sakamako daga bayanan farko da na biyu inda aka kammala harhada 10 cikin mazabu 11.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin abokan karatunsa

A baya mun ji cewa an tsaurara matakan tsaro a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta da ke jihar Kano.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan dakatar da hada sakamakon zabe da aka yi daga karamar hukumar Nasarawa saboda matsalolin tsaro. An sake karo wasu jami' an tsaro a hanyar Hajj Camp domin daidaita duk wani hatsaniya da ka iya kunno kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel