Kwamishinan 'yan sanda ya shiga ganawar sirrance da Kwamishinan zabe a jihar Kano

Kwamishinan 'yan sanda ya shiga ganawar sirrance da Kwamishinan zabe a jihar Kano

Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakil, ya shiga bayan labule a halin yanzu tare da babban Bature kuma Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu.

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, a halin yanzu ana can ana ci gaba da kus-kus tsakanin kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakil da kuma babban Bature kuma kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Shehu.

Ba bu masaniya dangane da dalilin wannan ganawa ta sirrance da ke wakana cikin gaggawa kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakil
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakil
Asali: Facebook

Sai dai manema labarai sun yi itifakin cewa, ganawar na gudana ne biyo bayan takaddama da kuma hargisti na siyasa da suka auku yayin da hukumar INEC ke tsaka da bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun bayyan cewa, an tsananta tsaro a fadin jihar Kano yayin da a halin yanzu dakarun soji da kuma jami'an tsaro na 'yan sanda da kuma masu jar kwala suka mamaye babban ofishin hukumar zabe ta kasa reshen jihar Kano daura da hanyar sansanin Alhazai.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, ganawar na gudana ne domin kulla dabaru da kuma tumke damarar tsananta tsaro a birnin Kano da kewaye yayin da ake gab da bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar da kuma 'yan majalisun dokoki.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sandan jihar Kano ta cikwikwiye Mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Kwamishinan kananan hukumomi na jihar, Murtala Sule Garo biyon bayan rudani da suka haifar yayin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar na karamar hukumar Nasarawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel