Sakamakon zabe: Gwamnan PDP ya lallasa abokin hamayyarsa na APC da kuri’u 709,334

Sakamakon zabe: Gwamnan PDP ya lallasa abokin hamayyarsa na APC da kuri’u 709,334

Aikin gama ya gama, inji masu iya magana, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da sunan gwamnan jahar Delta, Ifeanyi Okowa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya sake lashe zaben gwamnan jahar daya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Babban baturen zabe na jahar, Farfesa Seth Accra Jaja ne ya sanar da haka yayin daya sanar da sakamakon zaben a ranar Litinin, 11 ga watan Maris a garin Asaba, inda yace abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 215,938.

KU KARANTA: Bahallatsar zaben gwamnan jahar Kano: An jinjina ma kwamishinan Yansanda Wakili

Sakamakon zabe: Gwamnan PDP ya lallasa abokin hamayyarsa na APC da kuri’u 709,334
Okowa da Ogburu
Asali: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Farfesan yana cewa “A matsayina na babban baturen zabe, na tabbatar da an gudanar a zaben gwamna a jahar Delta a watan Maris, kuma yan takara da dama sun fafata, amma Ifeanyi Arthur Okowa na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben da samun kuri’u 925,272. Yayin da mai bi masa Cif Great Ogboru na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 215,938.”

A jawabinsa, yace akwai masu rajista zabe su miliyan biyu da dubu dari takwas da talatin da daya, da dari biyu da biyar (2,831,205), inda aka tantance mutane miliyan daya da dubu dari da tamanin da takwas da dari bakwai da tamanin da hudu (1,188,784) a ranar zabe.

Haka zalika an kada kuri’a miliyan daya da dubu dari da saba’in da takwas da dari uku da talatin da biyar, (1.188,784) sai kuma aka samu lalatattun kuri’u 24, 147, yayin da halastattun kuri’u suka tsaya akan 1,154,188.

Rahoton sakamakon zaben ya nuna Okowa ya lashe zabe a kananan hukumomi 23 cikin 25 na jahar, daga cikin kananan hukumomin da Okowa yafi samun kuri’a akwai karamar hukumar Warri ta kudu inda ya samu 139, 534, amma abokin hamayyarsa ya samu 10,906.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel