Yanzu Yanzu: Mukhtar Shehu na APC ya lashe zaben gwamna a Zamfara

Yanzu Yanzu: Mukhtar Shehu na APC ya lashe zaben gwamna a Zamfara

Dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, Alhaji Mukhtar Shehu, ya lashe zaben gwamna wanda ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris da ya gabata.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Alhaji Mukhtar Shehu, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Zamfara.

Baturen zabe na jihar, Farfesa Kabiru Bala na jami’ar Ahmadu Bello Zaria yace dan takarar na APC ya samu kuri’u 534,541 inda ya doke sauran abokan takararsa.

Yanzu Yanzu: Mukhtar Shehu na APC ya lashe zaben gwamna a Zamfara
Yanzu Yanzu: Mukhtar Shehu na APC ya lashe zaben gwamna a Zamfara
Asali: Facebook

Hakazalika babban abokin adawarsa na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) Dr. Bello Muhammad Mutawalle ya samu kuri’u 189,452.

KU KARANTA KUMA: Babu abunda zai samu sakamakon zaben gwamnan Kano - INEC

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Jam’iyyar APC a jihar Imo ta zargi gwamna Rochas da yin amfani da wasu jami’an tsaro wajen murde sakamakon zaben kujerar gwamna da aka yi a jihar ranar Asabar.

Jam’iyyar ta yi kira ga magoya bayanta da su saka ido a kan kuri’un da su ka kada domin ganin cewar gwamna Rochas bai samu damar murde sakamakon zabe don surukin sa ya zama gwamna ba.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Cif Marcelinus Nlemigbo, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a jihar. Nlemigbo ya yi kira ga hukumar soji da rundunar ‘yan sanda da su tsawatar wa da jami’an su don kar a yi amfani da su wajen aikata magudin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel