Bahallatsar zaben gwamnan jahar Kano: An jinjina ma kwamishinan Yansanda Wakili

Bahallatsar zaben gwamnan jahar Kano: An jinjina ma kwamishinan Yansanda Wakili

Biyo bayan bahallatsar data kunno kai a yayin da ake tattara alkalumman sakamakon zaben gwamnan jahar Kano a daren jiya 10 ga watan Maris, masu bibiyan al’amuran siyasar jahar Kano sun jinjina ma kwamishinan Yansandan jahar, Muhammad Wakili, bisa rawar da rundunar ta taka.

Ba kamar yadda aka saba samu a baya ba, inda ake samun hadin bakin Yansanda da yan siyasa, da sauran jami’an tsaro, da kuma hukumar zabe kanta wajen shirya manakisar siyasa, magudin zabe ko kuma aringizon kuri’u, kwamishina Wakili ya sha bambam, inji rahoton Legit.ng

KU KARANTA; Zaben gwamnan Kaduna: El-Rufai ya kammala kwantar da jam’iyyar PDP

Bahallatsar zaben gwamnan jahar Kano: An jinjina ma kwamishinan Yansanda Wakili
Muhammad Wakili
Asali: Facebook

Ga duk wanda ya kalli bidiyon yadda Yansanda suka kama mataimakin gwamnan jahar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna fita daga farfajiyar ofishin da ake tattara zaben karamar hukumar Nassarawa bayan ta tayar da hankali, da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sulen Garo, zaka san da gaske Yansanda ba wasa suka fito ba.

Dama dai tun kafin zaben ne aka jiyo jajirtaccen Dansanda Wakili, wanda aka fi sani da inkiya ‘Maza kwaya Mata kwaya’ a jahar Kano, yayi alkawarin zai yi aiki tsakaninsa da Allah, ba zai bari wani dan siyasa ya yaudareshi da kudi ba.

A jawabin da yayi a wata kafar sadarwa a kwanakin baya ya bayyana cewa bai taba amsan cin hanci ba, kuma yace babu wanda ya taba tunkararsa da batun cin hanci, kuma ma ko da an tunkareshi da batun cin hanci ba zai bada hadin kai ba.

Idan za’a tuna, kwamishina Maza kwaya Mata kwaya ya yi suna ne cikin wata hira da yayi a lokacin da yake kwamishinan Yansandan jahar Katsina, inda ya bayyana damuwarsa da yadda Maza da mata ke shan kwaya, manya da yara, tsofaffi da matasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel