Zaben Kano: Rundunar 'yan sanda ta sako Gawuna da Garo

Zaben Kano: Rundunar 'yan sanda ta sako Gawuna da Garo

Labarin da Legit.ng Hausa ta samu daga wata majiya mai tushe daga Kano na nuni da cewar rundunar 'yan sanda karkashin jagorancin kwamishina CP Muhammad Wakili ta saki mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, da kwamishinan kananan hukumomi, Nasiru Sule Garo.

Rundunar 'yan sanda ta kama manyan jami'an gwamnati biyu ne a daren jiya bayan sun yi kutse tare da kawo hayaniya a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamna a karamar hukumar Nassarawa.

Ana zargin mataimakin gwamnan da kwamishinan da yaga takardun sakamakon karamar hukumar Nasarawa da ake jira domin kammala tattara sakamakon zaben kujerar gwamna a matakin jiha.

Jihar Kano na da kananan hukumomi 44 kuma tuni sakamako daga kananan hukumomi 43 sun shiga hannun baturen zabe na jihar in banda karamar hukumar Nasarawa.

Zaben Kano: Rundunar 'yan sanda ta sako Gawuna da Garo
Gawuna a hannun jami'an 'yan sanda
Asali: Twitter

Jam'iyyar PDP ce a gaba a sakamakon kananan hukumomi 43 da su ka shigo hannu, sai dai babu tazara mai yawa tsakanin ta da jam'iyyar APC.

Batun yaga sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa ne ya jawo tsaiko wajen sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Mutanen jihar Jigawa APC su ka yi 'dodar'

Hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewar za ta koma matakin akwatin zabe da mazabu domin sake tattara sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa da za ta yi amfani da shi domin sanar da sakamako na karshe.

INEC ta ce za ta yi hakan ne a gaban wakilan jam'iyyu da ma su ruwa da tsaki a zaben gwamnan jihar da aka yi tun Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel