An tsaurara matakan tsaro a hedkwatar INEC a Kano

An tsaurara matakan tsaro a hedkwatar INEC a Kano

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta da ke jihar Kano.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan dakatar da hada sakamakon zabe da aka yi daga karamar hukumar Nasarawa saboda matsalolin tsaro.

An sake karo wasu jami' an tsaro a hanyar Hajj Camp domin daidaita duk wani hatsaniya da ka iya kunno kai.

An kuma dakatar da ziga-zigan ababen hawa da mutane a yankin yayinda ma' aikatan hukumar kadai aka bari su shiga da fita a wajen.

An tsaurara matakan tsaro a hedkwatar INEC a Kano
An tsaurara matakan tsaro a hedkwatar INEC a Kano
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, yanzu haka komai ya daidaita a jihar yayinda aka gano wasu mazauna yankin na gudanar da harkokin gabansu.

Sai dai an bude wasu wuraren kasuwanci harda bankuna, amma dai har yanzu kasuwannin Sabon gari da na rimi a rufe.

Wani mazaunin Sabon Gari, Mista Joseph Abdu yace watakila ba za a bude kasuwan sabon gari ba har sai INEC ta sanar da sakamakon zaben.

KU KARANTA KUMA: INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano

A wani lamari na daban, mun ji cewa Jam'iyyar Peoples Democratic Party ta nuna rashin amincewa da sakamakon zaben gwamna da ya gudana a jihar Kaduna a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Wakilin jam' iyyar, Mista Jerry Ishaya, wanda ya bayyana hakan a wajen hada kuri' u yace sakamakon ba gaskiyar kuri' un da aka kada bane.

Yace jam' iyyar tayi watsi da dukkanin sakamakon zaben baki daya.

Ishaya yayi bayanin cewa wakilan PDP a Zaria, Kabau, Kaduna ta arewa, Kaduna ta kudu, Igabi, Soba da Lere na jihar duk sun fada ma shugabancin jam' iyyar cewa ba a yi amfani da na' urara card reader ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel