Nicolos Felix yayi wata dabara ya samu kuri’u 110, 000 a zaben Shugaban kasa

Nicolos Felix yayi wata dabara ya samu kuri’u 110, 000 a zaben Shugaban kasa

Wani babban abu da ya ba jama’a mamaki a zaben bana shi ne yadda wani ‘Dan siyasa da bai shahara a Najeriya bai ya zo na uku a zaben shugaban kasan bana da aka yi makonni kadan da su ka wuce.

Nicolas Felix mai shekaru 37 shi ne ya zo bayan shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar na jam’iyyun APC mai mulki da PDP a zaben bana. Felix yayi takarar shugaban kasar ne a karkashin wata jam’iyya mai suna PCP.

Jam’iyyar ta Peoples Coalition Party ta samu kuri’u 110,196 ne a zaben, inda sauran ‘yan takarar da ake tunani za su tabuka wani abu irin su Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC, da Kingsley Moghalu YPP) da kuma Fela Durotoye.

Nicolas Felix wanda babu wanda ya san da shi, ya iya zuwa na uku ne a babban zaben kasar a dalilin jam’iyyar sa. Jam’iyyar ta PCP tana kusa da PDP ne a takardar kada kuri’a, wannan ya sa da-dama su kayi kuskuren zaben PCP.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ya lashe dukkanin hukumomin Jihar Katsina

Nicolos Felix yayi wata dabara ya samu kuri’u 110, 000 a zaben Shugaban kasa
‘Dan takarar PCP ya zo bayan Buhari da Atiku a zaben bana
Asali: UGC

Bayan kusancin PDP da jam’iyyar PCP a takardar kada kuri’a, haka zalika, take da alamar jam’iyyun adawar duk su na yanayi da juna. Ana tunanin dai wannan ne ya sa aka rika kuskuren zaben PCP da nufin kadawa PDP kuri’a a zaben.

Wannan ‘dan siyasa ya ba sauran ‘yan takaran bana mamaki domin kuwa idan aka tattara kuri’ar da Sowore, da Moghalu da Durotoye su ka samu bai haura 72, 000 ba, yayin da shi kadai ya samu mutum fiye da 100, 000 da su ka zabe sa.

Masana harkar siyasa dai sun ce jama’a ba su san wannan ‘dan takara ba, musamman idan aka fita daga cikin babban birnin tarayya Abuja. A zaben na bana, jam'iyyar ADC ce ta zo ta 4, sannan APGA ta zo ta 4.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel