Gwamnatina ba za ta sace dukiyar Kwara ba – Abdulrazaq ya dau alkawari

Gwamnatina ba za ta sace dukiyar Kwara ba – Abdulrazaq ya dau alkawari

Zababben gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq ya dau alkawarin cewa gwamnatinsa za ta kasance mai gaskiya ga mutane sannan ba za ta sace baitul malin jihar ba.

Abdulrazaq ya dauki alkawarin ne a daren ranar Lahadi a Ilorin inda ya gabatar da jawabin godiya a cikin magoya bayan jam’iyyar Progressive Congress (APC).

Taron ya samu halartan Mista Kayode Alabi, mataimakin zababben gwamnan Kwara, Alhaji Lai Mohammed ministan bayanai da al’adu kuma jigon APC a jihar da kuma Bashir Bolarinwa, Shugaban APC a Kwara da sauransu.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da Abdulrazaq na APC a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris a jihar.

Gwamnatina ba za ta sace dukiyar Kwara ba – Abdulrazaq ya dau alkawari
Gwamnatina ba za ta sace dukiyar Kwara ba – Abdulrazaq ya dau alkawari
Asali: UGC

Abdulrazaq ya samu kuri’u 331,546 inda ya kayar da babban abokin adawarsa Abdulrazaq Atunwa na Peoples’ Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 114,754.

APC ta lashe dukkanin kujerun majalisar dokokin jihar Kwara 24.

Abdulrazaq ya bayyana cewa mutanen Kwara sun gama Magana tunda APC ta lashe sama da kaso 70 cikin 100 na zaben da aka yi jihar sannan cewa gwamnati mai zuwa ba za ta taba basu kunya ba.

KU KARANTA KUMA: INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano

Ya koka akan halin da gwamnatocin baya suka sace albarkatun kasar inda suka jefa al’umman kasar cikin wani hali.

Zababben gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa sai ta ga abunda ya ture wa buzu nadi domin ganin yayiwa mutanensa aikin alkhairi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel