Har yanzu Buhari yaki cewa uffan game da bahallatsar zaben gwamnan jahar Kano

Har yanzu Buhari yaki cewa uffan game da bahallatsar zaben gwamnan jahar Kano

Duk da kwakwazon da zaben gwamnan jahar Kano ke sha a bakunan miliyoyin yan Najeriya, amma har yanzu ba’a ji koda uffan daga bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, duk kuwa da cewa jam’iyyar APC c eke rike da mulkin jahar Kano.

Haka nan ita uwar jam’iyyar APC ta kasa, ba’a ji duriyar shugabanta Adams Aliu Oshiomole ba, duk da cewa an sanshi baya barin kota kwana akan duk wani daya shafi bukatar jam’iyyarsa, hakan yasa jama’a na ta tunanin ko menene dalilin wannan shiru haka?

KU KARANTA: Zaben gwamnan Kaduna: El-Rufai ya kammala kwantar da jam’iyyar PDP

Har yanzu Buhari yaki cewa uffan game da bahallatsar zaben gwamnan jahar Kano
Gawuna a hannun Yansanda
Asali: Twitter

Legit.ng ta ruwaito tun a daren Lahadi, 10 ga watan Maris da hukumar zabe mai zaman kanta ta fara sanar da alkaluman sakamakon zabe ne aka yi ta samun cece kuce daga bangarorin biyu na siyasar jahar Kano, wadanda suke takarar gwamnan jahar, APC da PDP.

Idan za’a tuna jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dan takararta, yayin da PDP a karkashin tsohon gwamnan jahar, Rabiu Musa Kwankwaso ta tsayar da surukin Kwankwaso, Abba K Yusuf a matsayin dan takararta.

Sai dai ana cikin sanar da sakamako, inda baturen zabe ya sanar da sakamakon kananan hukumomi 43 cikin 44, sai kwatsam hargitsi ya tashi a sakatariyar hukumar INEC dake karamar hukumar Nassarawa, karamar hukumar da ta rage kacal kafin a kammala tattara alkalumma.

Mutane biyu da suka tayar da wannan rikici sune mataimakin gwamnan jahar, Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sulen Garo, inda rahotanni suka bayyana cewa Gawuna ya yaga takardar sakamakon zaben Nassarawa.

A dalilin wannan bahallatsa ne hukumar zabe mai zaman kanta ta dakatar da sanar da zaben na jahar Kano, inda tace har sai ta sake tattara alkalumman zaben karamar hukumar Nassarawa, kuma har lokacin hada wannan rahoto bata cigaba ba.

A yadda ake a yanzu Abba na jam’iyyar PDP ne ke kan gaba da kuri’u 951,531, yayin da Ganduje na APC keda kuri’u 935,451, bambamcin kuri’u 16,080 ne a tsakaninsu, hakan tasa wasu masana harkar zabe ke gudun kada a sake maimaita zabe a wasu rumfunan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel