INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano

INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta bayyana dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna na jihar Kano.

Babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe ne, Bello Shehu ya bayyana haka a yau Litinin, 11 ga watan Maris.

Hakan ya biyo bayan hargitsa cibiyar tattara sakamakon zaben Karamar Hukumar Nassarawa da ita kadai ta rage, da aka yi cikin daren jiya Lahadi. Inda aka yayyaga takardar sakamakon.

INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano
INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano
Asali: Twitter

Yace: “A lokacin da mu ke komawa mu ci gaba da tattara sakamako, sai muka samu labari maras dadi cewa an je Karamar Hukumar Nassarawa inda ake tattara sakamakon karamar hukumar, an hargisa wurin kuma an yayyaga takardun da ke dauke da sakamakon zaben da suka gudana a rumfuna da mazabu.

“A zaman yanzu dai babu wancan sakamakon zabe a hannun mu. Domin ma sai da ‘yan sanda suka kubutar da wasu mutane a wurin.

“Amma niyyar mu ita ce mu koma mu bi daki-dakin sakamakon da ke cikin na’urar tattara bayanan kuri’un da aka tara daga rumfuna da kowace mazaba."

A cewarsa idan suka yin haka ne za su bayyana sakamakon da doka ta amince a karba, da wanda doka ba ta amince a karba ba.

Jami’in tattara bayanai na jihar Kano, Farfesa Shehu ya ce ma’akatan sa na duba kuri’un da aka soke, wadanda ya ce suna da yawa.

Daga nan ya ce za su tantance a cikin kuri’in su gano yadda za a samu karancin su.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa

Ya ce ta haka ne za a iya gano wanda ya yi nasara.

Shi kuma Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, na Jihar Kano, yace a inda suka gano cewa akwai ko an yi zabe ba da ‘card reader’ ba, to sifili za a bayar a kawai a wuce wurin, a ci gaba da aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel