Jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa

Jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Injiniya Abdullahi Sule na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris a jihar Nasarawa.

Farfesa Abdullahi Bala, Baturen zaben ya sanar da Sule a matsayin zababben gwamna a ranar Litinin a Lafia bayan kamala hade-haden sakamakon zabe daga kananan hukumomi 13 da ke jihar.

Bala yace dan takarar na APC ya samu kuri’u 327,229 inda ya kayar da sauran abokan adawarsa.

A cewar shi, Mista David Ombugadu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri’u 184,281 yayinda Mista Labaran Maku na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya samu 132,784.

Jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa
Jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Nasarawa
Asali: UGC

Yace masu zabe 686,303 aka tantance, kuma 681,400 ne suka kada kuri’unsu a lokacin zaben.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’in PDP ya yaga takardar sakamakon zabe a Imo, yace Okorocha ne ya rubuta su

Bala ya ci gaba da bayanin cewa kuri’u 670,879 ne sahihai yayinda aka ki amincewa da 10,521.

Sakamakon ya nuna cewa APC ta lashe kananan hukumomi 11 cikin 13 da ke jihar yayinda Maku na APGA da Umar Aliyu Dona na Zenith Labour Party suka lashe Nasarawa Eggon da Doma.

A halin da ake ciki, wakilin PDP, Yakubu Dauda yaki sanya hannu akan sakamakon.

A cewarsa jam’iyyarsa ta kawo korafe-korafe da dama ga INEC kan tsarin gudanarwar zaben amma an yi watsi da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel