Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 13, PDP ta samu nasara a jahohi 9

Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 13, PDP ta samu nasara a jahohi 9

Duk da yake ba’a kammala tattara dukkanin alkalumman sakamakon zaben gwamnonin Najeriya daya gudana a karshen makon daya gabata ba, amma zuwa yanzu hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da wasu jahohin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu manya jam’iyyun siyasar Najeriya da kuma yan takarkarunsu sun san matsayinsu a wadannan jahohi da aka kammala sanar da sakamakonsu, inda a yanzu haka APC ke kan gaba da jahohi 13, yayin da PDP ke bi mata da jahohi 9.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta yi wuju wuju da PDP a kananan hukumomi 10 na jahar Zamfara

Daga cikin jahohin da jam’iyyar APC ta samu nasara sun hada da Legas, Gombe, Kwara, Kebbi, Nassarawa, Yobe, Neja, Katsina, Ogun, Jigawa, Kaduna, Borno da Zamfara, yayin da PDP ta dauke jahohin Abia, Cross Rivers, Taraba, Imo, Delta, Ebonyi, Enugu, Oyo da Akwa Ibom, kamar yadda INEC ta sanar.

Ga dai sunayen yan takarar da suka lashe zaben jihohinsu da kuri’un da suka samu kamar haka;

APC

Legas, Babatunde Sanwo Olu 739, 445

Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq 331, 546

Kebbi, Atiku Bagudu 673, 717

Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru 810, 993

Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya 364, 179

Neja, Abubakar Sani Bello 526,412

Katsina, Aminu Bello Masari 1, 178, 864

Nassarawa, Abdullahi Sule 327, 229

Yobe, Mai Mala Buni 444, 013

Ogun, Dapo Abioudun 241, 670

Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai 1,045,417

Zamfara, Mukhtar Shehu 534,541

Borno, Babagana Zulum 1,175,440

PDP

Oyo, Seyi Makinde 515, 621

Enugu, Ifeanyi Uguwanyi 449, 935

Akwa Ibom, Emmanuel Udom 519, 712

Ebonyi, David Umahi 393, 043

Abia, Okezie Ikpeazu 261, 127

Cross Rivers Ben Ayade 381,484

Delta Ifeanyi Okowa 925,272

Taraba, Darius Ishaku 520, 433

Imo, Emeka Ihedioha 273,404

Zuwa yanzu hukumar zabe tace zabe bai kammala a jihohin Filato, Sakkwato, Adamawa da Bauchi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel