An shiga rudani a Kano yayinda APC da PDP ke bikin samun nasara a lokaci guda

An shiga rudani a Kano yayinda APC da PDP ke bikin samun nasara a lokaci guda

Magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sun karade unguwannin Kano da murna, inda dukkanin bangarorin biyu ke ikirarin sun lashe zaben gwamna da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Har a lokacin da magoya bayan bangarorin biyu suka fita unguwanni don nuna farin cikin cewa sun ci zabe wato da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi dai ana kan hada sakamakon zaben ne.

An tattaro cewa an fara bukukuwan murna a fadin biranen jihar jim kadan bayan sakamakon zaben wanda ke nuna PDP a kan gaba ya karade shafukan zumunta.

Yayinda magoya bayan PDP ke murnar ganin sun kusa tsige gwamna mai mulki a jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, wadanda ke goyon bayan APC mai mulki ma sun fita yin murnar samun tazarce.

An shiga rudani a Kano yayinda APC da PDP ke bikin samun nasara a lokaci guda
An shiga rudani a Kano yayinda APC da PDP ke bikin samun nasara a lokaci guda
Asali: UGC

Sai dai, an lura cewa an tsaurara matakan tsaro a fadin birnin yayinda aka tura jami’an tsaro zuwa wurare daban-daban domin hana barkewar rikici a birnin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’in PDP ya yaga takardar sakamakon zabe a Imo, yace Okorocha ne ya rubuta su

A hedkwatar INEC ma an tsaurara matakan tsaro yayinda jami’an tsaro suka yiwa hanyar da ke sada mutun ga hedkwatar hukumar kawanya.

An kuma tattaro cewa wadanda aka tantance ne kadai ake bari su shiga ginin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel