Yanzu Yanzu: Jami’in PDP ya yaga takardar sakamakon zabe a Imo, yace Okorocha ne ya rubuta su

Yanzu Yanzu: Jami’in PDP ya yaga takardar sakamakon zabe a Imo, yace Okorocha ne ya rubuta su

Rahotanni sun kawo cewa tattara sakamako da ake daga zaben gwamna da aka gudanar a jihar Imo yak are da hargitsi bayan wani jami’in jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yaga takardar sakamakon zaben.

Harhada sakamakon wanda ke gudana a cibiyar tattara sakamako na INEC a IOwerri ya hadu da cikas bayan rikici ya kaure tsakanin jami’an jam’iyyar siyasa da ke kan gaba a jihar.

Rikicin ya fara ne lokacin da jami’in PDP, Uche Onyeaguocha, ya bayyana cewa ba za a sanar da sakamakon karamar uhukumar Ideato ta kudu ba.

Yayi zargin cewa Rochas Okorocha, gwamnan jihar, ya kori dukkanin jami’ai sannan ya rubuta sakamakon zaben don alfarma ga dan takarar da yake so.

Yanzu Yanzu: Jami’in PDP ya yagan takardar sakamakon zabe a Imo, yace Okorocha ne ya rubuta su
Yanzu Yanzu: Jami’in PDP ya yagan takardar sakamakon zabe a Imo, yace Okorocha ne ya rubuta su
Asali: Twitter

Amma dai jami’an sauran jam’iyyu sunce lallai sai a fadi sakamakon inda suka riki cewa sun rigada sun yi zanga-zanga a lokacin da aka ganatar da sakamakon karamar hukumar Aboh Mbaise.

Fransis Otunta, baturen zabe a jihar, bayan tattaunawa sai yace a fadi sakamakon.

Amma sai jami’in PDP yayi gaggawan zuwa kan teburin sannan ya yaga takardar sakamakon zaben.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisar Plateau ya mutu bayan ya lashe zabe

A ramuwar gayyawa, sai jami’in wata jam’iyya ma yayi gaggawan zuwa kan tebur sannan ya yaga sakamakon zaben sauran kananan hukumomi da aka riga aka harhada.

A halin da ake ciki, jami’an jam’iyyu, da jami’an zabe harda baturen zabe sun gudu daga cibiyar.

Jami’an yan sanda sun yi gaggawan kama jami’ai biyu da suka tarwatsa shirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel