Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka yan Boko Haram 40

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka yan Boko Haram 40

Dakarun rundunar hadaka ta Sojojin kasashen yankin tafkin Chadi, MNJTF, sun samu gagarumar nasara akan mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a wasu samame da suka kai musu da kuma karanbatta daban daban da suka yi tsakaninsu.

Kaakakin MNJTF, Kanal Timothy Antigha ne ya sanar da haka a daren Asabar, 9 ga watan Maris inda yace Sojojin sun kashe yan Boko Haram guda Arba’in a yayin dauki ba dadin da suka yi, hare haren da yace sun kwashe tsawon kwanaki goma suna kaiwa.

KU KARANTA; Akwai sake a zaben gwamnonin Adamawa, Sokoto, Bauchi da Filato – Inji INEC

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka yan Boko Haram 40
Makaman
Asali: Facebook

Timothy yace hadakan rundunonin Sojin sama dana kasa na kasashen Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya ne suka kai wannan mummunan hari akan mayakan Boko Haram a yankin tafkin Konduga dake tsakanin Nijar da Najeriya.

“A ranar Juma’a mayakan Boko Haram sun kai ma Sojoji hari a yankin Gueskerou dake tsakanin garin Diffa da kasar Nijar, sai dai dakarun basu yi kasa a gwiwa ba, inda suka mayar da wuta akan yan ta’addan, nan take suka kashe mutane 27, suka lalata motocin yaki 6, tare da kama makamai da dama.

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka yan Boko Haram 40
Makaman
Asali: UGC

“Haka zalika da misalin karfe 3 da 6 na ranar Asabar Sojoji sun sake yi arangama da yan ta’addan Boko Haram a yankin Abadam, anan ma mun kashe yan ta’adda 13, sa’annan mun kwace dimbin makamai da suka hada da bindigu da alburusai.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin yana cewa sun kama dan ta’adda guda daya, kuma sun kama babura guda 5, motocin yaki 3, nakiya guda uku da dai sauran kayayyakin yaki da yan Boko Haram ke amfani dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel