Dan majalisar Plateau ya mutu bayan ya lashe zabe

Dan majalisar Plateau ya mutu bayan ya lashe zabe

Mista Ezekiel Afon, wani dan majalisa mai wakiltan mazabar Pengana na jihar Kwara ya mutu yan sa’o’i kadan bayan yayi nasarar lashe zabe a mazabarsa.

Mista Bashir Sati, sakataren jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar ya tabbatar da mutuwar dan majalisan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Jos a ranar Lahadi.

A cewar Sati, Afon ya mutu a yammacin ranar Lahadi bayan yar gajeruwar rashin lafiya.

“Abun bakin ciki ne cewa mun rasa Afon, daya daga cikin jajirtattun mambobin jam’iyyarmu kuma jajirtaccen dan majalisa bayan an kaddamar da shi a matsayin wanda ya sake lashe zaben kujerarsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: A yanzu haka yan bindiga na nan suna kone-konen gidaje a Kaduna

“Koda dai dama bashi da lafiya na dan wani lokaci amma labarin mutuwarsa ya jefa mu cikin juyayi,” inji shi.

An fara zabar Afon a majalisar dokoki karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a 2015 amma ya sauya sheka zuwa APC a 2017.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel