Yanzu-yanzu: Ofishin INEC na ci da wuta a Imo

Yanzu-yanzu: Ofishin INEC na ci da wuta a Imo

Ofishin hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC dake karamar hukumar Ngor Okpuala na jihar Imo na ci wuta bal-bal a yanzu haka.

Wasu yan baranda ne suka fasa inda ma'aikatan INEC ne hada sakamakon zaben gwamna da yan majalisar dokokin jihar misalin karfe 2 suka tayar da hankali.

Wata majiya ta bayyana cewa yan barandan sun fittitike jami'an tsaron da wajen kafin suka bankanwa ofishin wuta.

Da wuri jami'an yan sanda suka kawo agaji ga ma'aikatan hukumar INEC dake Imo da kuma kayayyakin zabe.

Shugaban hukumar INEC na jihar Imo, Francis Ezeonu ya ce shikenan an tayar da rigima a unguwar.

Kasance tare da mu domin cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Online view pixel