Yanzu Yanzu: A yanzu haka yan bindiga na nan suna kone-konen gidaje a Kaduna

Yanzu Yanzu: A yanzu haka yan bindiga na nan suna kone-konen gidaje a Kaduna

Rahotanni sun kawo cewa a yanzu haka wasu yan bindiga na nan suna kone-konen gidaje a kauyen Angwan Barde, karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.

Wani jigon garin da ya nemi a boye sunansa ya fada ma jaridar TheCable cewa maharan na a hanyarsu na komawa wani garin da ke kusa bayan sun kai farmaki Angwan Barde.

Harin na zuwa ne kasa da kwanki 12 bayan an kashe mutane 40 da kuma kona gidaje da dama a kayen Karamai, duk a karamar hukumar Kajuru da ke jihar.

Yace kashe-kashen ya fara ne inda aka kai wa wasu manoma a yankin hari a ranar Asabar.

Yanzu Yanzu: A yanzu haka yan bindiga na nan suna kone-konen gidaje a Kaduna
Yanzu Yanzu: A yanzu haka yan bindiga na nan suna kone-konen gidaje a Kaduna
Asali: UGC

Yakubu Sabo, Kakakin yan sandan jihar Kaduna, bai amsa kiran wayarsa ba inda aka aika masa sakon waya kan lamarin.

Harin farko da aka fara kaiwa Angwan Barde ya kasance a ranar Juma'a, 11 ga watan Fabrairu, lokacin da wasu da ake zargin makaiyaya ne suka kai farmaki kauyen da tsakar dare sannan suka kashe mutane 11.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan takarar APC, Abdulrazaq ya lashe dukkanin kananan hukumomi 16 a jihar Kwara

Harin ya yi sanadiyar wasu hare-haren ramuwar gayya sannan mutane da dama sun mutu. Gwamna Nasi El-Rufai ya bayyana adadin wadanda suka mutu a matsayi 130.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel