Zamfara: INEC ta dage zaben Gwamna da Majalisa a Shinkafi

Zamfara: INEC ta dage zaben Gwamna da Majalisa a Shinkafi

Hukumar zabe mai zaman-ta na kasa watau INEC ta dakatar da zabe a wasu wurare a cikin karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara. Matsalar rashin tsaro ne yasa dole aka fasa zaben a jiya Asabar.

INEC ta bada sanarwar cewa ta dage zabe a wasu Kauyuka da ke cikin Shinkafi bayan wani hari da wasu tsagera su ka kai ya sa an gaza gudanar da zaben gwamna a jiya. Jami’in hokumar a Zamfara, Garba Galadima ya fadi wannan.

Galadima ya fadawa jaridar PREMIUM TIMES dazu da safe cewa za a shirya zaben ne a wani lokacin daban a halin yanzu. Garin Shinkafi da Zurmi yana cikin inda tsageru su ka tasa a gaba da kashe-kashe a cikin kwanakin nan.

KU KARANTA: 'Yar Takarar APC tayi wa PDP war-was a Kudancin Kaduna

Zamfara: INEC ta dage zaben Gwamna da Majalisa a Shinkafi
INEC ta dakatar da zaben Gwamna a wani Kauyen Zamfara
Asali: Facebook

Inda za a gabatar da sabon zabe sun hada da cikin Unguwar Kwari da ke cikin karamar hukumar Shinkafi. Akwai rumfuna 10 a cikin Kwari sannan kuma akwai Unguwar Kurya, inda a nan ma ake da akwatunan zabe har 9 inji INEC.

Dama can mun ji labari cewa ‘dan takarar APC mai mulki a zaben gwamnan da za ayi, ya samu nasarar lashe akwatin mazabar sa. Mukhtar Shehu Idris ya samu kuri’a 1, 131 a akwatin sa da ke cikin Tudun Wadan Garin Gusau a Zamfara.

A akwatin ‘dan takarar gwamnan na APC, jam’iyyun adawa ba su iya samun komai ba. Bello Matawalle na PDP da kuma Bala Bello duk samu kuri’a 1 rak ne a kaf wannan rumfar a zaben na jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel