Yanzu-yanzu: APC ta lashe kujeru 3 cikin 6 a Abuja, ana sauraron sakamakon sauran

Yanzu-yanzu: APC ta lashe kujeru 3 cikin 6 a Abuja, ana sauraron sakamakon sauran

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 3 cikin 6 dake birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda kuka sani, ba'a gudanar da zaben gwamna a birnin tarayya amma ana na kananan hukumomi da kujerun kansiloli. A yanzu, hukumar ta bayyana cewa babu matsaya a zaben karamar hukumar Kuje da Bwari.

Jam'iyyar All Progressives Congress ta lashe dukkan kananan hukumomi uku da aka sanar zuwa yanzu:

Gwagwalada

Mustapha Adamu Danza (APC) - 21,960

Abubakar Giri (SDP) - 14,105

AMAC

Abdullahi Adamu Candido (APC) - 53,753

Vivian Anazodo (PDP) - 35,753

Abaji

Abdulrahman Ajiya (APC) - 13,442

Muhammad Ashafa (APC) - 10,473

KU KARANTA: Sakamakon zaben kujerar gwamna a jihohin Borno, Adamawa da Yobe

Alkaliyar zaben karamar hukumar Bwari, Zainab Gbefwi ta bayyanawa manema labarai cewa ba'a cimma matsaya ane saboda rikicin da ya faru da unguear Rubochi.

Mrs Gbefwi ta ce an yi watsi da kuri'u a Kwaku da Kabi saboda an ki amfani da na'urar Card reader; sannan an lalata kayan INEC sannan aka jiwa ma;aikatan INEC rauni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel