An hallaka Jami’an tsaro da Ma’aikatan zabe a Jihar Katsina

An hallaka Jami’an tsaro da Ma’aikatan zabe a Jihar Katsina

Mun ji cewa Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun tabbatar da kisan da aka yi wa wani jami’in su guda a jihar Katsina a lokacin da ake zaben gwamna da kuma ‘yan majalisar dokoki a jihar jiya Ranar Asabar.

Rundunar ‘Yan Sanda da ke Katsina ta bayyana cewa an kashe wani jami’in ta, sannan kuma an yi awon-gaba da wasu Ma’aikatan zabe har 3 a yayin da ake gudanar da zabe a jihar. Kakakin ‘Yan Sandan jihar ya fadi wannan jiya.

‘Dan sanda SP Gambo Isa, a wasu jawabai da ya saki, ya fadawa Duniya cewa wasu ‘yan bindiga sun yi wa wasu ‘Yan sanda kwantan-bauna a cikin Unguwar Gobirawa da ke cikin Garin Falale a cikin karamar hukumar nan ta Danmusa.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun ji babu dadi a hannun Dakarun Najeriya

An hallaka Jami’an tsaro da Ma’aikatan zabe a Jihar Katsina
An kashe ‘Dan Sanda guda a wani Kauye a cikin Katsina
Asali: Original

Babban Jami’in da ke magana da yawun ‘yan sandan na Katsina ya bada tabbacin cewa a sanadiyyar wannan hari da aka kai ne aka hallaka wani kurtun ‘dan sanda mai suna Cpl Mannir Usman, yana tsakiyar aikin zabe.

Haka zalika wadannan ‘yan bindiga da su ka kai wa motar ‘yan sandan hari, sun sace wasu Ma’aikata da aka tura yankin domin aikin zabe. Wannan dai duk ya faru ne a sa’ilin da aka hallaka wannan karamin jami’in na ‘yan sanda.

Rundunar ‘yan sanda na Katsina sun kuma bayyana cewa an harbe wani jami’in tsaro na hukumar NSCDC a kirji. Shi kuma wannan mummunan abu ya faru ne a cikin Kauyen Santar Amadi a karamar hukumar Kankara, a jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel