Yanzu-yanzu: An kai harin kunar bakin wake Adamawa da safe nan

Yanzu-yanzu: An kai harin kunar bakin wake Adamawa da safe nan

Wani harin Bam a Shuwa dake jihar Adamawa da safiyar Lahadi, 10 ga watan Maris, 2019 ya hallaka akalla mutane biyu.

Ana zargin yan kungiyar Boko Haram da kai wannan hari ta hanyar amfani da roka kwana daya bayan zaben gwamnar jihar.

Mai unguwan Dihu, Mohammed Sanusi, ya bayyanawa manema labarai cewa wasu mata yan kunar bakin biyu sukayi nufin kai hari wani waje amma bam din ya fashe kafin su isa manufarsu.

Yace: "An tayar da Bam a Shuwa. Yan kunar bakin biyuu ne suka kai hari. Wata yar karamar da harin ya shafa tana asibitin Shuwa. Yan mata masu kunar bakin waken sun yi niyyar kai hari ga masu zuwa coci ne amma bam din ya fashe da su kafin isa cocin."

"Akwai yiwuwan cewa wasu bama-bamai da basu tashi ba na wajen amma jami'an tsaro na kokarin ganosu."

KU KARANTA: Yadda zaben kujerar gwamna da yan majalisu ke gudana a jihohin Gombe, Bauchi da Flato

Mun kawo muku rahoton cewa cewa an ji harbe-harbe a Garin Manchok da ke cikin karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna a jiya Ranar Juma’a yayin da ake gab da zaben gwamnoni.

Kamar yadda labari ya zo mana, an ji harbin bindigogi a wani harin fashi da aka kai a cikin Garin na Manchok. Wasu masu fashi da makami ne su ka burma wani shagon da ake dillacin kudi da kimanin karfe 9:30 na daren jiya.

Jama’a da-dama dai sun tsere a lokacin da aka ji harbe-harben bindigogin ko ta ina a cikin gari inda kowa yake neman inda zai fake. Wannan ya sa har ma’aikatan zabe da ke aiki a yankin su ka tsere domin gudun a hallaka su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel