Boko Haram: Sojojin Najeriya sun ragargaza ‘Yan ta’adda a Ngwom

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun ragargaza ‘Yan ta’adda a Ngwom

A makon jiya ne Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa sun sha karfin wasu ‘Yan Boko Haram a kusa da Kauyukan Ngwom da kuma Kubu da ke cikin Jihar Borno. Sojojin sun yi nasarar ruguza lagon ‘yan ta’addan a karon da aka yi.

Sojojin na Najeriya sun yi wani karon-batta da ‘yan ta’adda a Yankin Ngwom a Ranar Laraba da ta wuce, inda su ka yi nasarra karbe manyan makamai a hannun su. Daga cikin makaman da su ka fito daga hannun 'Yan ta'addan akwai:

1. Katuwar bindiga mai kabo jirgin sama

2. Bindigogin gurnet har guda 2

3. Da kuma Bindigogi kirar AK-47 har 5

Kanal Sagir Musa wanda shi ne mukaddashin mai magana da yasun sojin Najeriyar ya bayyana wannan inda yace dakarun kasar sun hallaka wasu ‘yan ta’addan da-dama yayin da wasu kuma su ka sha da kyar su ka ari na kare.

KU KARANTA: An bindige wani 'Dan Majalisar Najeriya har lahira a Oyo

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun ragargaza ‘Yan ta’adda a Ngwom
Kadan daga cikin makaman da sojojin Najeriya su ka karbe
Asali: Facebook

Haka kuma dazu nan mu ka ji cewa rundunar hadin-gwiwar sojojin Afrika watau MNJTF sun koyawa wasu ‘yan Boko Haram darasi bayan da su kayi masu rubuti a yankin rafin Kamadogou da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

Babban Jami’in sojin da ke magana da yawun Dakarun na MNJTF da ke N'Djamena ta kasar Chad watau Timothy Antigha ya bayyana irin nasarar da su ka samu hannun ‘yan ta’addan a jiya, wanda su ka hada da:

1. Hallaka ‘Yan ta’adda 23

2. Karbe AK-47 guda 20 da wasu manyan bindigogi 47

3. Makamin AA na harbin jirgin sama har guda 5

An dai kuma samu cafke wani ‘Dan Boko Haram da ran sa ban da kuma manyan bindigogi masu lugade da aka samu a hannun ‘yan ta’addan da abubuwan hawa da aka ruguza a kan iyakar na Nijar da Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel