Sakamakon Zabe: Hukumar 'yan sanda ta gargadi al'umma kan gudanar da bikin murna a jihar Kano

Sakamakon Zabe: Hukumar 'yan sanda ta gargadi al'umma kan gudanar da bikin murna a jihar Kano

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta gargadi magoya bayan jam'iyyun siyasa na jihar akan gudanar da bikin murna da bilinbituwar bayyana farin cikin gabanin bayyanar sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jiya Asabar.

A yayin da a jiya Asabar, 9 ga watan Maris, aka gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokoki cikin jihohi 29 da ke fadin kasar nan, mun samu cewa sakamakon zaben ya fara bayyana wasu kafofi na watsa labarai da zaurukan sada zumunta.

Tun gabanin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta kammala kididdiga da tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar Kano, wani rukuni na siyasar Kano ya fara bayyana murnar da aiwatar da bikin farin cikin samun nasara.

Sakamakon Zabe: Hukumar 'yan sanda ta gargadi al'umma kan gudanar da bikin murna a jihar Kano
Sakamakon Zabe: Hukumar 'yan sanda ta gargadi al'umma kan gudanar da bikin murna a jihar Kano
Asali: Twitter

A sanadiyar haka hukumar 'yan sandan jihar da sanadin kakakin ta, Haruna Abdullahi, ta gargadi al'ummar jihar kan kauracewa aiwatar da makamancin wannan lamari na bilinbituwar bikin murna gabanin bayyanar sakamakon zaben a sahihance daga hukumar INEC.

Yayin murza gashin baki da daga gashin gira, hukumar ta yi gargadin cewa, akwai yiwuwar wannan lamari zai haddasa rudani tare da haifar barazana ga zaman lafiya da kuma kwanciyar hankalin al'umma a birnin Kano da kewaye.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito cewa, kawowa yanzu ba bu sakamakon zaben kowace karamar hukuma da hukumar INEC ta kammala tattarawa cikin kananan hukumomi 44 da jihar Kano ta kunsa.

Cikin yunkurin ta na daukar mataki domin sauke nauyin da rataya a wuyan ta na tabbatar da tsaro, hukumar 'yan sandan jihar Kano ta ce ba za ta saurara ba wajen cafke duk wanda ta riska cikin wannan lamari mai barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel