Jiga-Jigan Najeriya da su ka samu nasara karo na farko a zaben Majalisar Dattawa

Jiga-Jigan Najeriya da su ka samu nasara karo na farko a zaben Majalisar Dattawa

Biyo bayan babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, 'yan siyasa da dama a fadin kasar nan sun samu narasa ta lashe zaben majalisar tarayya domin wakilcin mazabun su a zauren majalisar dattawa.

Jiga-Jigan Najeriya da su ka samu nasara karo na farko a zaben Majalisar Dattawa
Jiga-Jigan Najeriya da su ka samu nasara karo na farko a zaben Majalisar Dattawa
Asali: Depositphotos

Duk da cewa wannan shine karo na farko da za su dandana kujerar majalisar dattawa, sun kasance kwararrun 'yan siyasa ta fuskar madafan iko da suka rika a baya ka ma daga kujerun gwamna, majalisar wakilai da sauran mukamai daban-daban.

Binciken jaridar Daily Trust ya tattaro muku jeranto na sunayen dukkanin wadanda suka yi nasara karo na farko yayin zaben majalisar dattawa da aka gudanar makonni biyu da suka gabata. Ga jerin su tare da shiyoyin da za su ci gaba da wakilta bayan an rantsar da su a ranar 29 ga watan Mayu kamar haka:

1. Ibrahim Yahaya Oloriegbe (Kwara ta Tsakiya)

2. Orji Uzor Kalu (Abia ta Arewa)

3. Kashim Shettima (Borno ta Tsakiya)

4. Tanko Almakura (Nasarawa ta Kudu)

5. Ibrahim Geidam (Yobe ta Gabas)

6. Rochas Okorocha (Imo ta Yamma)

7. Ibrahim Shekarau (Kano ta Tsakiya)

8. Abubakar Shehu Tambuwal (Sokoto ya Kudu)

9. Dayo Adeyeye (Ekiti ta Kudu)

10. Lola Ashiru (Kwara ta Kudu)

11. Ifeanyi Ubah (Anambra ta Kudu)

12. Christopher Ekpeyong (Akwai Ibom Arewa maso Yamma)

13. Ubah Sani (Kaduna ta Tsakiya)

14. Suleiman Abdu Kwari (Kaduna ta Arewa)

15. Ibrahim Hassan Hadejia (Jigawa Arewa maso Gabas)

16. Binos Yero (Adamawa ta Kudu)

17. Ishaku Cliff (Adamawa ta Arewa)

18. Akon Eyakenyi (Akwa Ibom ta Kudu)

19. Yakubu Oseni (Kogi ta Tsakiya)

20. Ibrahim Muhammad Bomai (Yobe ta Kudu)

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

21. Umar Sadiq (Kwara ta Arewa)

22. Abba Moro (Benuwe ta Kudu)

23. Kola Balogun (Oyo ta Kudu)

24. Amos Bulus (Gombe ta Kudu)

25. Muhammad Sani Musa (Neja ta Gabas)

26. Bima Muhammad Enagi (Neja ta Kudu)

27. Nicholas Tofowomo (Ondo ta Kudu)

28. Kabir Barkiya (Katsina ta Tsakiya)

29. Bello Mandiya (Katsina ta Kudu)

30. Tolu Odebiyi (Ogun ta Yamma)

31. Ajibola Bashiru (Osun ta Tsakiya)

32. Adenigba Fadahunsi (Osun ta Gabas)

33. Lere Oriolowo (Osun ta Yamma)

34. Michael Ama Nnachi (Ebonyi ta Kudu)

35. Bayo Osinowo (Legas ta Gabas)

36. Ikra Ali Bilbis (Zamfara ta Tsakiya)

37. Adamu Bulkachuwa (Bauchi ta Arewa)

38. Sandy Onor (Cross River ta Tsakiya)

39. Hezekich Dimka (Filato ta Tsakiya)

KARANTA KUMA: Kwamishinan 'yan sanda ya shiga ganawar sirrance da Kwamishinan zabe a jihar Kano

40. Biobarakuma Degi Eremmenyo (Bayelsa ta Gabas)

41. Lawrence Eurudjiakpo (Bayelsa ta Yamma)

42. Ezenwa Onyebuchi (Imo ta Gabas)

43. Barry Npigi (Ribas Kudu maso Gabas)

44. Opeyemi Bamidele (Ekiti ta Tsakiya)

45. Halliru Dauda Jika (Bauchi ta Tsakiya)

46. Diri Douye (Bayelsa ta Tsakiya)

47. Beti Apiafi (Ribas ta Yamma)

48. Istifanus Dung Gyang (Filato ta Arewa)

49. Abdulaziz Yari (Zamfara ta Yamma)

50. Gabriel Suswam (Benuwe Arewa maso Gabas)

51. Aishatu Dahiru (Adamawa ta Tsakiya)

52. Godiya Akwashiki (Nasarawa ta Arewa)

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel