'Yan ta'adda sun kai wa Mataimakin Gwamnan jihar Kano hari, an dakatar da bayyana sakamakon zabe

'Yan ta'adda sun kai wa Mataimakin Gwamnan jihar Kano hari, an dakatar da bayyana sakamakon zabe

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito, an samu tsaikon bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Kano biyo bayan harin da masu ta'ada suka kai wa mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna da kuma Kwamishinan kananan hukumomi na jihar, Murtala Sule Garo.

Mataimakin Gwamna tare da Murtala Garo sun tsallake rijiya baya ta wani mummunan harin miyagu yayin yunkurin kwantar da hankalin magoya bayan su biyo bayan rudanin da masu ta'ada suka haddasa yayin tattara sakamakon zabe na karamar hukumar Nasarawa.

Rahotanni kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito sun bayyana cewa, Gawuna wanda ya kasance dan asalin karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano ya yi gamo da azal yayin isowa domin kwantar da hankalin magoya baya a harabar tattara sakamakon zaben Mahaifar sa.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna
Asali: Facebook

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, hukumar jami'an tsaro ta 'yan sanda ta yi gaggawar kai masu ceto inda a halin yanzu suke fake a babban ofishin ta da ke Unguwar Bompai a birnin Kanon Dabo.

Sai dai wata majiyar rahoton ta bayyana cewa, Mataimakin gwamnan tare da kwamishinan na kananan hukumomin jihar Kano sun shiga hannun jami'an tsaro yayin yunkurin su na kawo rudani ana tsaka da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar a hedikwatar karamar hukumar ta Nasarawa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kawowa yanzu hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC,ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 43 cikin 44 na dukkanin garin Kano da kewaye yayin da ya rage ta bayyana sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Jaridar ta fahimci cewa, sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa zai tabbatar da rinjayen nasara tsakanin dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma dan takara na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Biyo bayan wannan hargitsi tare da rudani da ya auku yayin tattara sakamakon zaben karamar hukumar ta Nasarawa, ya sanya hukumar INEC ta dakatar da bayyana sakamakon zaben jihar Kano da cewar sai tarzoma ta lafa kuma kowa ya samu nutsuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel