Yanzu-yanzu; An bindige dan majalisar wakilan tarayya har lahira

Yanzu-yanzu; An bindige dan majalisar wakilan tarayya har lahira

Dan majaisar wakilan tarayaa mai wakiltan mazabar Lagelu/Akinyele a jihar Oyo, Hanarabul Temitope Olatoye Sugar, ya rasa rayuwarsa da yammacin nan.

Mun samu rahoton cewa an garzaya dashi asibitin jami'ar Ibadan bayan wasu yan baranda sun bindigeshi a birnin jihar.

Kakakin asibitin jami'ar Ibadan UCH, Toye Akinrilola, ya tabbatar da cewa an kawo dan majalisan asibitin cikin mumunan hali bayan an harbesa a fuska.

Likitocin da ke cikin sashen jinyar gaggawa sunyi iyakan kokarinsu wajen cecen rayuwarsa amma ya kwanta dama. Ya mutu yana mai shekaru 47.

KU KARANTA; Sakamakon zaben kujerar gwamna a jihohin Borno, Adamawa da Yobe

Yanzu-yanzu; An bindige dan majalisar wakilan tarayya har lahira
Yanzu-yanzu; An bindige dan majalisar wakilan tarayya har lahira
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa akalla mutane uku sun rasa rayukansu da safiyar ranar zabe a jihar RIvers, kuku maso kudancin Najeriya.

Wani matashi mai sune Micheal Abednego, ya gamu da ajalinsa ne a hannun wani jami'in dan sanda a karamar hukumar Ahaoda ta yamma dake jihar.

Hakazalika, wata jigor jam'iyyar APC da a'a gano sunanta ba har yanzu da wani matashi suna rasa rayukansu a karamar hukumar Ndoni, Ogba/Egbema.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel