Fayose ya gaza cin akwatin sa a jihar Ekiti

Fayose ya gaza cin akwatin sa a jihar Ekiti

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC ta lashe zabe a akwatin zaben tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da ke Afao Ekiti a karamar hukumar Ifelodun da ke Jihar.

Dan takarar jam'iyyar APC a mazabar Irepodun/Ifelodun ta 2, Alhaji Hakeem Jami'u ya lallasa abokin hamayarsa na jam'iyyar Peoples Democratic Party’s candidate, Sunday Omosilade inda ya samu kuri'u 168 shi kuma Omosilade ya samu kuri'u 26 a rumfar zaben makarantar frimare na St David da ke Afao Ekiti.

Omosilade wanda hadimin Fayose ne ya aike wa Hukumar Zaba Mai Zaman Kanta INEC wasika a ranar 1 ga watan Maris inda ya nemi janyewa daga takarar.

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ke gudana a Sokoto, JIgawa da Kebbi

Fayose ya sha kaye a hannun APC a jihar Ekiti
Fayose ya sha kaye a hannun APC a jihar Ekiti
Asali: Depositphotos

Sai dai INEC ta ba amince da bukatarsa ba saboda wa'addin da doka ta bayar na cewa duk mai son janyewa daga zabe zai iya yin hakan ne a kalla kwanaki 45 kafin zabe.

Kazalika, a rumfunan zabe masu lamba 15 da 003 a gundumar Igbemo, Jami'u ya samu 171 da 335 yayin da takwararsa na jam'iyyar PDP ya bai samu ko kuri'a guda ba a rumfunann zaben biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel